Isa ga babban shafi
Najeriya

Dimokuradiyya: Buhari ya koka kan tsaikon zartas da hukuncin kotuna

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koka bisa tafiyar hawainiyar dake addabar tsarin mulkin Dimokaradiya ta fuskar shari’a, ganin yadda ake daukar dogon lokaci kafin yanke hukunci.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Twitter/Asorock
Talla

Buhari wanda ya cika shekaru 77 da haihuwa a ranar talata, ya bayyana haka ne yayin zantawa da kafar talabijin din kasar ta NTA.

Yayin zantawar, shugaban Najeriyar yace a lokacin da ya dare kan jagorancin kasar a zamanin mulkin soja, ya tattara masu rike da mukaman gwamnati da ake zargi da yashe dukiyar al’umma zuwa gidan Yari, tare da shaida musu cewar, dukkaninsu masu laifi ne, sai dai wanda ya kare kansa daga zargin da ake masa a gaba kotu.

Buhari ya kara da cewar a waccan lokacin ya kafa kwamitocin bincike a kusan dukkanin shiyyoyin Najeriya, domin tantance laifi ko gaskiyar shugabannin da ake tuhuma da aikata ba dai dai ba, kuma wadanda aka gano cewar sun mallaki abinda yafi karfin halastattun kudaden da suke samu, an mayarda kudaden da suka yashe zuwa baitulmalin gwamnati.

Kafin zantawar ta ranar talata da Buhari yayi da NTA, a baya shugaban Najeriyar ya koka, kan wasu matakai ko tsare-tsaren dimokaradiya, da ya ce basu da muhimmaci, amma tilas yake bin tsare-tsaren, saboda gudun yiwa mulkin dimokaradiyyar karan tsaye.

Wadannan kalamai na shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da wasu al’ummar kasar ke zargin sa da kin bin umarnin kotuna, abinda ya kai ga jaridar Punch tace daga yanzu, za ta dinga kiran sa a matsayin Janar Muhammadu Buhari, sabanin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.