Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta fi far wa Musulmai fiye da Kirista- Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, kashi 90 na mutanen da rikicin Boko Haram ya rutsa da su Musulmai ne, sabanin tunanin wasu da ke ganin, kungiyar na daukar Kiristoci a matsayin loman farko a hare-harenta.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Shugaban ya fadi haka ne a wani shafin bayanna ra’ayoyian baki mai taken “Speaking Out” a Mujallar Christianity Today.

A cikin maudu’in shugaban mai taken “Buhari: Ya kamata imanin Fasto Andimi ya zaburar da daukacin ‘yan Najeriya”, shugaban ya jinjina wa fasto Lawan Andimi da Boko Haram ta kashe shi saboda ya ki fita daga addininsa na Kirista.

A wani bangare na rubutun, shugaba Buhari ya tunatar da jama’a cewa, akwai Musulmai a cikin ‘yan matan makarantar Chibok da Boko Haram ta sace.

Ya kara da cewa, mayakan na Boko Haram sun sace fiye da dalibai mata 100 kuma daya ce daga cikinsu Kirista.

Kazalika kungiyar ta kaddamar da hare-haren a Masallatai tare da kashe wasu fitatun limamai guda biyu a cewar Buhari.

“A takaice, wadannan ‘yan ta’adda da ke gab da shan-kasa na kai farmaki kan raunana da masu addinai da marasa addinai da karami da babba ba tare da banbancewa ba.” Inji Buhari.

Shugaban ya jaddada cewa, kungiyar ta Boko Haram na shure-shuren mutuwa a yanzu, yana mai cewa, ba za su bari kungiyar ta raba kawunan Musulmi da Kirista ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.