Najeriya
Mun mayar da hankali kan yaki da ta'addanci-Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari y ace, gwamnatinsa ta mayar da ciakken hankali wajen yaki tare da kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga da ta’addanci a kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Buhari ya bayyana haka ne a birnin Addis Ababa na Habasha a yayin wata ganawa da shugabannin Kwamitin Kula da Al’ummar Najeriya da ke rayuwa a Habasha.
Shugaba Buhari ya roki ‘yan Najeriya da su mara baya ga hukumomin tsaron kasar da ke aikin tabbatar da hadin kan kasa.
A yayin gudanar da taron, an yi shiru na minti daya domin karrama mutanen da Boko Haram ta kashe a ranar Litinin a jihar Borno.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu