Isa ga babban shafi

MDD zata tallafawa Arewacin Najeriya da dala miliyan 182

Hukumar Samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da gidauniyar tara Dala miliyan 182 domin tallafawa mazauna yankin arewa maso gabashin Najeriya da rikicin Boko Haram ya shafa na watanni 6 masu zuwa.

Buhunan kayan abinci da hukumar ke rabawa kasashe matalauta
Buhunan kayan abinci da hukumar ke rabawa kasashe matalauta AFP PHOTO / ROBERTO SCHMIDT
Talla

Hukumar a sanarwar da tayi mai dauke da sanya hannun Kelechi Onyemaobi tace tana bukatar kudaden cikin gaggawa domin kai dauki ga miliyoyin mutanen da rikicin tare da annobar coronavirus ta shafa.

Sanarwar tace hukumar ta damu matuka da halin da irin wadannan mutane ke ciki a Jihohin Adamawa da barno da Yobe wadanda ke fuskantar tsananin yunwa, yayin da wasu ke cikin yanayin gobe da nisa.

Hukumar ta bayyana yankin a matsayin daya daga cikin yankunan duniya dake fuskantar matsalar aikin jinkai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.