Isa ga babban shafi
Najeriya-Ta'addanci

Babu bambamci tsakanin IPOB, OPC da Boko Haram - Dambazau

Tsohon Ministan Cikin Gidan Najeriya, Laftanal-Janar. Abdul-Rahman Dambazau mai ritaya ya ce babu abin da ya raba kungiyoyin yarbawa ta OPC da na haramtattun Biafra IPOB da takwararsu ta mayakan Boko Haram a tsattsauran ra’ayi.

Tsohon Ministan Cikin Gidan Najeriya, Laftanal-Janar. Abdul-Rahman Dambazau mai ritaya.
Tsohon Ministan Cikin Gidan Najeriya, Laftanal-Janar. Abdul-Rahman Dambazau mai ritaya. © The Guardian
Talla

Dambazau ya bayyana haka ne yayin gabatar da kasida a Kwalejin koyan Yakin Soja da ke Abuja ga mahalarta taron.

Tsohon ministanm ya yi zargin cewa kungiyoyin biyu suna daukar nauyin wani sabon salon tsattsauran ra'ayi da ka iya kunna wutar rikicin kabilanci ta yadda za su cimma burinsu na raba Najeriya.

Dambazau ya ce ‘yan sanda suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen dakile fitintinun da ke faruwa a duk fadin kasar,“ a maimakon barin komai ga sojoji ”.

“Kungiyoyin biyu suna ta kokarin ganin sun kunna wutar rikice-rikicen kabilanci a duk fadin kasar ta hanyar kazamin harin da suke kaiwa kan mazauna arewacin musamman ‘ yan kasuwar da ke kudu a matsayin hanyar hanzarta cimma burinsu na raba Najeriya.

“Muna ganin kamanceceniya tsakanin Boko Haram da Indigenous People of Biafra (IPOB) da Oodua People’s Congress (OPC) dukkaninsu kungiyoyin ne na tsattsauran ra’ayi. Dukkanin kungiyoyin uku suna aiki ne a kan tsarin tsattsauran ra'ayi, "in ji Dambazau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.