Isa ga babban shafi
Najeriya

Yan bindiga sun kashe 'Yan Sanda 3 a jihar Deltan Najeriya

'Yan Bindiga da ake zaton magoya bayan kungiyar IPOB dake fafutukar kafa kasar Biafra ne a Najeriya sun kai hari tashar Yan Sandan Umutu dake Jihar Delta inda suka kashe jami’an tsaron guda 3.

Taswirar Najeriya
Taswirar Najeriya RFI
Talla

Edafe Bright, mai magana da yawun rundunar Yan Sandan Jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin wanda yace ya faru ne a cikin daren juma’a.

Bright yace anyi musayar wuta tsakanin Yan bindigar da ake zargin sun je satar makamai ne da jami‘an Yan Sanda wadanda suka yi nasarar kashe biyu daga cikin su.

Wata bindiga mai daukar alburusai 50.
Wata bindiga mai daukar alburusai 50. AFP - STEFAN HEUNIS

Kakakin Yan Sandan yace sun yi asarar jami’an su guda biyu a musayar wutar, yayin da wani mai rike da mukamin ASP kuma ya rasu a asibiti sakamakon hawan jini.

Hare haren Yan bindigar a Yankin kudu maso gabas da kudu maso kudancin Najeriya sun yi sanadiyar kashe Yan Sanda 127 a watanni 4 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.