Gwamnatin Najeriya ta dakatar da Twitter
Gwamnatin Najeriya ta dakatar da shafin Twitter a kasar, inda ta ce, ana amfani da dandalin sada zumuntar wajen wargaza hadin kan al’ummar kasar.
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar Yada Labarai da Al'adu ta Najeriya ta ce, an dakatar da Twitter ne har sai baba ta gani bayan ta zarge shi da taka rawa a fafutukar mayakan Biafra masu neman ballewa a yankin kudu maso gabashin kasar.
Wannan na zuwa ne kwanaki biyu da shafin ya goge sakon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a shafinsa.
A shafin nasa, shugaba Buhari ya ce
Akasarin wadanda ke wuce gona da iri a yau, matasa ne da ba su da masaniya kan asarar rayukan da aka samu a lokacin yakin basasar Najeriya. Mu da muka kwashe watanni 30 a fagen-daga, za mu fahimtar da su ta hanyar da ta dace .
Sai dai kamfanin na Twitter ya share wadannan kalamai na Buhari, yana mai cewa, hakan ya saba wa ka’idojinsa, sannan kuma ya samu korafe-korafe daga jama’a.
A yayin mayar da martani, Ministan Yada Labarai na Najeriya Lai Mohamed ya ce, cikin ruwan sanyi, shafin na Twiiter ya kawar da kai daga kalaman Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB da mukarrabansa.
Minisatan ya ce, Twitter ya kawar da kai daga kalaman Kanu da ke tunzira kashe-kashen jami’an ‘yan sanda, sannan kuma ya nuna son-kai a yayin zanga-zangar ENDSARS, lokacin da matasa suka lalata tare da sace kadarorin gwamnati da sunan ‘yanci.
Ministan ya ce, ya yi mamakin yadda kamfanin ke kallon kalaman Buhari a matsayin masu tayar da hankula.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu