Amurka ta caccaki gwamnatin Najeriya saboda dakatar da Twitter
Amurka ta soki lamirin gwamnatin Najeriya a game da dakatar da dandalin sada zumunta na Twitter a kasar, tana mai bayyana matakin a matsayin sako mara armashi ga al’umar kasar da ma masu zauba jari a cikinta.
Wallafawa ranar:
A wata sanarwa, ofishin jakadancin Anmukra a Najeriya ta ce kundin tsarin mulkin kasar ya bai wa kowa damar fadin albarkacin baki.
Fadar gwamnatin Najeriya ta kare haramcin da ta yi wa Twitter, tana mai cewa dandalin Twitter ya dade yana tabargaza a kasar kuma ba a daukar mataki
A wata sanarwa da ya fitar a Asabar dinnan, kakain fadar gwamnatin, Malam Garba Shehu ya ce gwamnatin Buhari ba za ta zura ido kamfanonin sadarwa su wargaza kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu