Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun fara karbar horo daga Boko Haram - Rahoto

Jami'ai a Najeriya sun yi gargadin cewa ‘yan ta’adda da ke da alaka da kungiyar IS suna horas da gungun ‘yan bindiga da ke yin garkuwa da mutane a yankin arewa maso yammacin kasar, alamar da ke nuna zurfafar hadin gwiwa tsakanin bangarorin masu dauke da muggan makamai.

Wata bindiga mai daukar alburusai 50.
Wata bindiga mai daukar alburusai 50. AFP - STEFAN HEUNIS
Talla

Masu bibiyar lamurran da ke wakana sun bayyana faragaba kan yadda hadin gwiwar ‘yan ta’addan zai sake dagula barazanar tsaron da jami'an tsaron Najeriya ke fafutukar murkushewa tsawon shekaru, a sassan yankin arewa masu gabashi da kuma arewa maso yammacin kasar.

Cikin wata wasika da shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya Muhammad Babandede ya aikewa jami’ansa a ranar 23 ga watan Yuli wadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya samu, Babandede ya yi gargadin cewa 'yan ta'adda masu yawa daga Zamfara na kwarara zuwa yankin Borno don samun horo daga mayakan Boko Haram, dan haka ya zama dole su sa ido tare da daukar matakan dakile barazanar.

'Yan bindiga sun addabi arewa maso yammacin Najeriya

Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya ya dade yana fama da gungun ‘yan bindiga masu aikata miyagun laifuka wadanda ke kai hare -hare kan kauyuka, suna sace mutane da kisan gilla tare da kona gidaje bayan sace dukiya.

Matakan tura sojoji da kuma kulla yarjejeniyar zaman lafiya sun gaza kawo karshen hare-haren da 'yan fashin dajin masu sansanoni a dazukan da suka ratsa jihohin Katsina, Kaduna, Zamfara da kuma Neja.

A watannin baya bayan nan ne kuma gungun ‘yan bindigar suka maida hankali wajen satar daliban makarantu domin karbar makudan kudade a matsayin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.