Isa ga babban shafi

Gwamnatin Najeriya ta gaza wajen samarwa jama’a tsaron da ya kamata-Amnesty

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana takaicin ta game da gazawar gwamnatin tarayyar Najeriya na samarwa jama’ar kasar tsaron da ya kamata.Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wani rahoto da ta fitar, game da yanayin da tsaro ke ciki a Najeriyar.

Wata bindiga mai daukar alburusai 50.
Wata bindiga mai daukar alburusai 50. AFP - STEFAN HEUNIS
Talla

A cewar Amnesty International cikin wata guda kadai an kashe mutane 112 a rikice-rikicen da aka samu a jihohin Kaduna da Plateau a Najeriyar.

Arewacin Najeriya
Arewacin Najeriya Audu Marte AFP/Archivos

Kungiyar cikin rahoton da ta fitar ta ce baya ga mutanen da suka hallaka dalilin rikice-rikicen, masu garkuwa da mutane sun kuma sace wasu 160.

Amnesty din ta kuma kara da cewa an kuma samu tashin rikici tsakanin Fulani da makiyaya da ya lashe rayukan mutane da dama.

Kungiyar ta kare hakkin dan Adam ta kuma ce da alama gwamnatin Najeriya bata wani yunkuri na tabbatar da tsaro a kasar, la’akari da yadda ake sace mutane baji ba gani, yayin da ‘yan ta’adda ke kaiwa kauyuka hare-hare kusan kullum da kuma kisan kan mai uwa da wabi.

Rahoton na Amnesty ya kuma jadadda cewa akalla mutane 78 aka kashe yayin da aka yi garkuwa da 160 tsakanin 3 ga watan Yuli zuwa 5 ga watan Agusta a jihar Kaduna cikin su kuma har da 121 na makarantar Bethel Baptist.

Nigeria
Nigeria AFP

A jihar Plateau kuma mutane 34 aka kashe 7 daga cikin su makiyaya a ranar 1 ga watan Yuli a garin Dogon Gaba sai Fulani biyu da aka kashe a kauyen Fusa lokacin da suke kan hanyar su ta neman shanun su da suka bata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.