Isa ga babban shafi
Najeriya

Masu garkuwa, sun sako mahaifiyar mai horar da kungiyar kwallon kafar Najeria Samson Siasia

Mahaifiyar mai horarda kungiyar kwallon kafar tarayyar Nigeria a gasar cin kofin kwallon kafa, a wasanni Olympique Samson Siasia, cewa da Mme "Ogere Siasia, ta kubuta daga hannun yan tsageran da su ka yi garkuwa da ita a yankin kudancin kasar, kamar yadda majiyar yan sanda ta sanar a yau lahadi.  

Samson Siasia sabon Kociyan Nigeria
Samson Siasia sabon Kociyan Nigeria
Talla

A cikin sanarwar da Kakakin ma’aikatar yan sandan Anisim Butswat ya karanta ya ce, Mahaifiyar ta Samson Siasia, da yan tsagera suka yi garkuwa da ita tun ranar 16 ga watan November suna masu neman a biyasu diyya, a safiyar jiya assabar ne, aka ganota a wata hanya dake cikin jahar Bayalsa inda yan tsageran suka sake ta a gefen Titi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.