Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Mutanen Sokoto dubu 50 suka gudu Nijar saboda matsalar tsaro - Dan Majalisa

Akalla mutane sama da dubu 50 daga karamar hukumar Sabon Birni dake Jihar Sokoton Najeriya suka tsallake iya zuwa Jamhuriyar Nijar domin samun mafaka sakamakon tabarbarewar tsaro ganin yadda Yan bindiga ke kai musu hari suna kasha su ba tare da kaukautawa ba.

Gwamnan jihar Sokoto kuma shugaban gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya Aminu Waziri Tambuwal
Gwamnan jihar Sokoto kuma shugaban gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya Aminu Waziri Tambuwal © Twitter / @AWTambuwal
Talla

Dan majalisar Jihar Sokoto dake wakilatar yankin Aminu Almustapha Boza ya bayyana haka inda yake cewa wadannan mutane da suka fito daga garuruwa 17 yanzu haka sun samu mafaka a kauyukan Tudun Sunnah da Gidan Runji dake karamar hukumar Maradi.

Boza yace akalla mutane sama da 300 Yan bindiga suka kashe a karamar hukumar Sabon Birni kawai daga bara zuwa bana.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar Boza yayi zargin cewar yayi iya bakin kokarin sa domin ganin gwamnan jihar su Aminu Waziri Tambuwal domin gabatar masa da rahoto akan irin ukubar da mutanen yankin sa ke fuskanta amma abin yaci tura.

Dan majalisar yace gwamnan yaki yarda ya bashi damar ganin sa ba tare da bayyana masa dalilin haka ba, yayin da yankin da yake wakilta ya zama dandalin ayyukan ta’addanci a jihar.

Yan bindiga a Najeriya
Yan bindiga a Najeriya © Daily Trust

Boza ya bayyana takaicin sa na shiga harkokin siyasa da kuma irin goyan bayan da suka baiwa gwamnan lokacin sake takarar sa sakamakon alkawarin da yayi na cewar zai tabbatar musu da tsaro da kuma ci gaban yankin su.

Dan majalisar yace rabon gwamnan da zuwa yankin su domin ganewa idanun sa halin da suke ciki tun bara da ‘yan ta’adda suka kashe mutane da dama a Yankin Terah, inda ya gargade su akan daukar makamai domin kare kan su.

Sai dai a nashi martani Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yayi watsi da wannan matsayi inda yace yana tintibar dan majalisar akan matsalar tsaron da ta addabi yankin na sa.

Gwamnan yace ko a baya ya shirya ganawa tsakanin dan majalisar da kwashinan yan sanda da kuma daraktan hukumar tsaron farin kaya ta DSS inda suka bashi damar tintibar su a koda yaushe da zaran an samu matsala.

Sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya. premiumtimesng

Mai magana da yawun gwamnan yace dan majalisar na daga cikin yan majalisu biyu da aka gayyata taron tsaron da akayi a wannan mako amma shi bai je ba sai na karamar hukumar Isa ne ya halarci taron.

Gwamnan yace ko a ranar alhamis ya kira dan majalisar kafin barin sa Sokoto, amma kuma dan majalisar ya musanta batun gayyatar duk da amincewa cewar sun yi Magana da ta waya a ranar alhamis.

Boza yace abinda Tambuwal ya fada masa shine ya shaidawa Ministan Yan Sanda da shugaban kwamitin tsaro a Majalisar Dattawa, Sanata Aliyu Wamakko da Sanata Ibrahim Gobir da kuma shugaban sojin kasan Najeriya halin da ake ciki a yankin, amma yace shi ba zai yi ba domin ba shine babban jami’in tsaron jihar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.