Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Sau 50 boko haram na neman hallaka ni - Zulum

Gwamnan Jihar Borno dake Najeriya Babagana Umara Zulum ya bayyana cewar akalla ya tsallake rijiya da baya sama sau 50 sakamakon hare haren da kungiyar boko haram ke kai masa domin neman hallaka shi bayan sun kashe Yan Jihar Barno sama da dubu 100.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum © Buhari Sallau
Talla

Yayin ganawa da manema labarai bayan ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a Abuja, Zulum yace rikicin boko haram na shekaru 12 yayi sanadiyar mutuwar mutanen jihar Barno sama da dubu 100, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Gwamnan ya sanar da cewar ya zuwa yanzu mayakan boko haram 2,600 suka tuba, suka kuma mika kan su a jihar, cikin su harda mata da kananan yara.

Gwamna Zulum yana yiwa shugaba Buhari bayani akan tubabbun boko haram tare da Ibrahim Gambari
Gwamna Zulum yana yiwa shugaba Buhari bayani akan tubabbun boko haram tare da Ibrahim Gambari © Buhari Sallau

Zulum yace daga cikin mutanen akwai wadanda da karfi aka kama su aka kuma saka su daukar makamai domin yiwa kungiyar yaki, cikin su harda yara kanana.

Gwamnan yace gwamnatin sa bata tunanin baiwa tubabbun mayakan koda sisin kwabo saboda aje makaman su, yayin da yace ya gana da shugaban kasa akan makomar su da kuma bayyana dalilin da zai sa a karbe su a cikin al’umma.

Tubabbun mayakan boko haram dake neman afuwa
Tubabbun mayakan boko haram dake neman afuwa © Daily Trust

Ya zuwa wannan lokaci ana ci gaba da tafka mahawara akan makomar tubabbun, yayin da wasu ke bukatar ganin an gurfanar da su a gaban shari’a domin amsa tambayoyi, wasu na cewa ya dace a horar da su domin sauya tunanin su da kuma sanya su cikin al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.