Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Nasarorin Buhari ba za suyi tasiri ba muddin babu tsaro - Dan Majalisa

Wani ‘Dan Majalisar wakilan Najeriya Yusuf Adamu Gagdi yace duk kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari na bunkasa noma da yaki da cin hanci da rashawa da gina hanyoyin jiragen kasa ba za suyi tasiri ba muddin ya kasa samarwa ‘Yan Najeriya da tsaron da suke bukata domin gudanar da harkokin su na yau da kullum.

Dan Majalisa Yusuf Adamu Gagdi
Dan Majalisa Yusuf Adamu Gagdi © Yusuf Gagdi
Talla

Gagdi dake wakiltar mazabar Kanam da Kanke da Pankshin daga Jihar Plateau a Majalisar dokokin ya bayyana haka ne a budadiyar wasikar da ya rubutawa shugaba Buhari domin janyo hankalin sa akan zub da jini da kuma kashe kashen da ake samu a sassan kasar.

‘Dan Majalisar wanda ya fito jam’iyya guda da shugaban yace kundin tsarin mulki ya basu dama a matsayin su na ‘Yan Majalisu wajen janyo hankalin shugaban kasa domin gudanar da ayyukan da suka dace da kuma nuna masa inda ya dace yayi gyara idan bukatar haka ta taso.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gawmnan Plateau Simon Lalong
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gawmnan Plateau Simon Lalong © Nigeria presidency

Gagdi ya bayyana matukar damuwar sa akan yadda Yan bindiga ke kashe mutane a garuruwan dake cikin Najeriya ba tare da daukar matakin kare lafiyar su, yayin da rikici tsakanin makiyaya da manoma ke kara zafafa, tare da satar dalibai da kona garuruwa, a daidai lokacin da jami’an tsaron da ake saran zasu kare lafiya da dukiyoyin jama’a suka gaza gudanar da ayyukan su kamar yadda suka dace.

‘Dan majalisar yace ya bada shawarwari da dama a matsayin sa na wakili da kuma kudirorin da Majalisar wakilai ta gabatar sama da 200 akan yadda za’a tinkari matsalar tsaro a Najeriya amma gwamnati ta gaza amfani da su.

Gagdi yace hakki ne a wuyar su a matsayin su na wakilai su gabatar da bukatun jama’a da kuma koken su akan halin da suka samu kansu, kuma wannan ne dalilin da ya sa ya rubutawa shugaban kasa budadiyar wasika domin jan halin sa da kuma makusantar sa akan halin da jama’a suke ciki da kuma bukatar yin gyara cikin lokaci.

Alamun Yan bindiga
Alamun Yan bindiga © Depositphotos

‘Dan Majalisar yace shi da jama’ar da yake wakilci basu yarda da shirin gwamnati na taimakawa ‘Yan ta’adda da tubabbun boko haram ba, alhali mutanen da suka rasa gidaje da gonakin su na zama a matsayin ‘Yan gudun hijira ba tare da gwamnati ta tallafa musu ba.

Dangane da rikicin jihar Plateau, Gagdi yace ya bada shawarwari da dama a matsayin sa na tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Plateau kuma tsohon shugaban kwamitin zaman lafiya akan hanyoyin da suka dace abi wajen tabbatar da zaman lafiya da kawo karshen rikice rikicen da ake samu tsakanin makiyaya da manoma, amma banda gwamnatin jihar Plateau da ta aiwatar da nata hurumin, gwamnatin tarayya tayi watsi da nata nauyin.

Daga cikin shawarwarin da suka gabatar yace akwai h kafa kwamitin zaman lafiya da hukumar sasanta jama’a da karfafa rundunar tsaron jihar Plateau ta ‘Operation Rainbow’ da kuma taimakawa wadanda rikici ya ritsa da su, amma har ya zuwa yanzu gwamnatin tarayya bata taimakawa jihar ba wajen sauke nauyin dake kan ta, musamman bada naira biliyan 10 da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi alkawari a shekarar 2018 domin sake tsugunar da mutanen da rikicin jihar ya shafa a kananan hukumomi da dama.

Sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya. premiumtimesng

Gagdi yace abin takaici ne yadda wasu ke ganin gazawar Gwamnan jihar Simon Bako Lalong wajen tabbatar da zaman lafiya, inda ya bayyana cewar a shekarun da suka gabata babu wata gwamnatin Jihar da ta jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar kamar wannan wadda aka kwashe shekaru 6 ba tare da samun wata matsala mai girma ba.

Dan majalisar ya bada shawarar hukunta duk wadanda aka samu suna da hannu wajen haddasa rikice rikice ko a ina suke a fadin Najeriya da kuma raba ofishin rundunar samar da zaman lafiya ta jihar da runduna ta 3 ta sojojin Najeriya da kuma hadin kai tsakanin hukumomin tsaro wajen aiki tare a matsayin hanyoyin da za’a inganta tsaro a jihar da kuma Najeriya baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.