Isa ga babban shafi
Najeriya

An yi watsi da ayyuka fiye da dubu 13 a yankin Neja Delta - Rahoto

Ministan kula da Harkokin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio ya ce rahoton binciken da aka yi kan Hukumar Ci gaban yankin na Neja Delta NDDC, ya nuna cewa akwai ayyuka sama da dubu 13 da aka yi watsi da su a yankin.

Mukaddashin shugaban Hukumar Raya Yankin Niger Delta, Daniel Pondei da ya yanke jiki ya fadi a zauren Majalisar Wakilan Najeriya.
Mukaddashin shugaban Hukumar Raya Yankin Niger Delta, Daniel Pondei da ya yanke jiki ya fadi a zauren Majalisar Wakilan Najeriya. Daily Trust
Talla

Sanata Akpabio ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Abuja, lokacin da ya mika rahoton binciken ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta hannun ministan shari’a, Abubakar Malami.

Akpabio ya ce tun kafin gabatar da rahoton wasu ‘yan kwangila suka koma kan aikin su da kan su, kuma kawo yanzu sun kammala ayyukan hanyoyi kusan 77.

Shugaban na hukumar NDDC, yankin Neja Delta na ci gaba da zama koma baya tun daga shekarar 1958, duk da kokarin gwamnatocin baya ta hanyar kirkirar shirye -shirye da ayyuka daban-daban domin bunkasa yankin.

A halin da ake ciki dai, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatin sa za ta tabbatar ta kwato sama da Naira tiriliyan 6 da ake zargin an karkatar da su a yayin gudanar da ayyukan hukumar NDDC tsakanin shekarar 2001 zuwa 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.