Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Ana laluben dimbim kudade da suka bace a hukumar bunkasa Niger Delta

A Najeriya, masu bincike na kokarin gano yadda aka yi da wasu kudade da suka kai biliyoyin daloli da ake zargin an sace su a hukumar bunkasa yankin Niger Delta, bayan zaman bin bahasi da majalisar dokokin kasar ta yi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. businessday
Talla

Kamar bangaren man fetur na kasar, ana daukar hukumar da aka kirkiro don bunkasa yankin Niger Delta mai arzikin man fetur da kasancewa wata daba ta rashawa da kwanciyar magirbi kan dukiyar al’umma tun kafuwarta shekaru 20 da suka wuce.

Jihohi 9 na kasar na samun tiriliyoyin nairori duk shekara daga hukumar bisa sahalewar doka.

Wani bincike da majalisar dokokin kasar ta gudanar na nuni da cewa ya zuwa yanzu, ayyuka sama da dubu 12 ne da aka bayar, amma kalilan daga cikinsu ne aka kammala.

A wannan shekarar kadai, fiye da naira biliyan 81 ne suka bace bat, inda ake zargin ko jami’an hukumar sun yi kwanciyar magirbi a kai ko kuma ‘yan kwangila sun lamushe ba tare da aiwatar da ayyukan da aka basu ba.

Wasu damasheren kudaden ma, cewa aka yi an tura jami’ai horo a kasashen waje a daidai lokacin da duniya ke a garkame sakamakon bullar annobar coronavirus.

Duk da dimbim arzikin man fetur da iskar gas da ke wannan yankin na Neja Delta, talauci da fatara sun mai kanta, lamarin da ya janyo rikicin ‘yan tsagera a farkon shekarun 2000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.