Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TATTALIN ARZIKI

Akalla jihohin Najeriya 30 ke fuskantar barazanar talaucewa

Akalla Jihohin Najeriya 30 ake saran zasu durkushe sakamakon rashin samun kudaden harajin VAT ganin yadda Jihohin Rivers da Lagos ke kokarin karbe harajin da ake samu daga jihohin su maimakon saka su cikin asusun tarayya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria presidency
Talla

Wannan ya biyo bayan wani hukuncin kotu da ya baiwa Jihar Rivers damar karbar kudin harajin kai tsaye maimakon gwamnatin tarayya wadda take rabawa jihohi da kananan hukumomi kowanne wata.

Harajin VAT na taimakawa gaya wajen samarwa gwamnatoci kudaden haraji daga jama’a wanda ke fitowa daga cinikayyar da mutane keyi, kuma ko a shekarar 2019 irin wannan haraji na VAT ya bada gudumawar da ta kai sama da kashi 16 na kudaden harajin da Najeriya ta samu.

Gwamnan Rivers Nyesom Wike ya umurci kamfanonin dake Rivers da su fara biyan Jihar sa harajin VAT
Gwamnan Rivers Nyesom Wike ya umurci kamfanonin dake Rivers da su fara biyan Jihar sa harajin VAT Daily Trsut

Akasarin jihohin Najeriya sun dogara ne da kudaden da suke samu daga gwamnatin tarayya wajen gudanar da manyan ayyuka da kuma biyan albashin ma’aikata, sabanin jihohi irin su Lagos da Rivers wadanda ke bada gudumar akalla kashi 70 na kudaden harajin VAT da ake tarawa a asusun tarayya.

Tuni wadannan jihohi guda biyu na Rivers da Lagos suka umurci majalisun su da suyi doka wadda zata basu karfin karbar harajin maimakon gwamnatin tarayya, matakin da ake ganin zai yi matukar illa ga zaman tarayya wajen tara haraji da kuma raba shi ga jihohin Najeriya 37.

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya bukaci majalisar dokokin jihar da ta dauki mataki irin na Rivers wajen yin dokar karbar harajin VAT
Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya bukaci majalisar dokokin jihar da ta dauki mataki irin na Rivers wajen yin dokar karbar harajin VAT © LASG

Wannan mataki na su ya biyo bayan hukunci wata kotun tarayya dake Fatakwal wadda tace jihohi ne ya dace su karbi harajin VAT amma ba gwamnatin tarayya ba.

Tuni shugaban hukumar tara kudaden haraji na kasa Muhammad Nami ya kalubalanci hukuncin kotun, ya kuma bukaci majalisar dokokin Najeriya da ta yiwa dokar karbar harajin VAT gyaran fuska yadda zai ci gaba da zama hannun gwamnatin tarayya maimakon jihohi.

Masana tattalin arziki na cewar wannan rikici wata dama ce ga sauran jihohin Najeriya akalla 30 da basa iya tara kudaden harajin da ya dace da su farka daga bacci domin lalubo hanyoyin da zasu bunkasa kudaden shigar da suke samu domin gudanar da ayyukan raya kasa.

Shalkwatar babban bankin Najeriya CBN a birnin Abuja.
Shalkwatar babban bankin Najeriya CBN a birnin Abuja. REUTERS/Afolabi Sotunde

Masanan sun ce muddin aka ci gaba da tafiya yadda ake yi yanzu jihohi da dama ba zasu iya gudanar da manyan ayyuka da kuma biyan ma’aikatan su ba, sakamakon raguwar kudaden shigar da zasu fuskanta.

Daga cikin jihohin da ake ganin suna iya tsayawa da kafafuwan su akwai Lagos da Rivers da Akwa Ibom da Kaduna da kuma Kano saboda kyakyawan tsarin da suke da shi na tara kudaden haraji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.