Isa ga babban shafi
Najeriya-Ilimi

An kashe malaman boko 2,295 a arewa maso gabashin Najeriya

Asusun Bunkasa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa, an kashe malaman makarantun boko dubu 2 da 295 a yankin arewa maso gabashin Najeriya a cikin shekaru 11 da aka kwashe ana fama da rikici a yankin.

Hare-haren ta'addanci sun yi zagon-kasa ga bangaren ilimi a arewa maso gabashin Najeriya.
Hare-haren ta'addanci sun yi zagon-kasa ga bangaren ilimi a arewa maso gabashin Najeriya. UNICEF
Talla

An dai yi wa malaman kisan gilla ne tsakanin 2009 zuwa 2020.

Shugabar Ofishin Asusun mai kula da shiyar jihar Borno ta Najeriya, Phuong Nguyen ta bayyana haka a wata hira ta musamman da jaridar Premium Times albarkacin zagayowar ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin nazari game da kare bangaren ilimi daga fuskantar hare-hare a sasaan duniya.

Kwararriyar Jami’ar wadda ta yi aiki a wasu kasashen duniya da suka yi fama da tashe-tashen hankula ta ce, hare-haren ta’addanci sun yi zagon-kasa ga fannin ilimi a yankin arewa maso gabashin Najeriya, yayin da aka lalata makarantu dubu 1 da 400, sannan kuma aka tilasta wa sama da yara miliyan 1 kaurace wa azuzuwansu.

Wannan matsalar ta ta’addanci ta tilasta wa hukumomi rufe makarantun boko daga watan Disamban 2013 zuwa watan Yunin 2015 a jihar Borno, yayin da a Yobe da Adamawa, aka rufe makarantun na wani kankanin lokaci.

Wasu mayakan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
Wasu mayakan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya. AFP

jami’ar ta UNICEF ta ce, hare-haren makamai da rikcin kabilanci da bala’o’i da kuma tabarbarewar tattalin arziki duk sun dada fadada gibin da ake da shi a Borno  da Adamawa da Yobe dangane da ilmantar da yara kanana.

Alkaluma sun nuna cewa, kashi 52 cikin 100 na yaran da ke tsakankanin shekarun shiga makaranta a matakin farko, ba su taba halartar makarantar ba a yankin arewa maso gabashin Najeriya, adadin da aka bayyana a matsayin mafi girma a Najeriya, idan aka kwatanta da sauran yankunan kasar.

Rikcin Boko Haram ya tilasta wa miliyoyin mutane kaurace wa muhallansu, lamarin da ya sa aka sama musu matsuguni na wucean-gadi a sansanonin 'yan gudun hijira.

Boko Haram ta sace daliban makarantar Chibok a shekarar 2014
Boko Haram ta sace daliban makarantar Chibok a shekarar 2014 HO AFP/File

Matalsar ta gudun hijira ta haifar da cikas ga kananan yara musamman ma ga 'ya mace wajen neman ilimi, la’akari da nauyin da ya karu a kanta na kula da iyalanta da kuma aikace-aikacen gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.