Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

An kashe shugaban kungiyar ISWAP Al-Barnawi- Rahotanni

Rahotanni daga Najeriya sun ce an kashe shugabann kungiyar ISWAP Abu Mus'ab Al-Barnawi a Jihar Borno, daya daga cikin kungiyoyin da ke kai munanan hare hare suna kashe jama'a a yankin Tafkin Chadi.

Shugaban tsagin kungiyar Boko Haram ISWAP da ke biyayya ga kungiyar IS Abu Musab Al-Barnawi
Shugaban tsagin kungiyar Boko Haram ISWAP da ke biyayya ga kungiyar IS Abu Musab Al-Barnawi Guardian Nigeria
Talla

Bayanan dake fitowa daga Najeriyar sun ce an kashe Abu Musab Al-Barnawi ne a karshen watan Agustan da ya gabata kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar.

Rahotanni masu karo da juna na nuna cewa sojojin Najeriya ne suka kashe shi, yayin da wasu majiyoyi kuma ke cewa a rikicin cikin gida ya mutu.

Ya zuwa wannan lokaci sojojin Najeriya basu sanar da kashe shugaban na kungiyar ISWAP ba.

Shidai Al-Barnawi ‘da ne ga Muhammadu Yusuf, mutumin da ya kafa kungiyar boko haram kafin jami’an tsaron Najeriya su kashe shi a shekarar 2009 lokacin da ya kaddamar da yaki akan su, abinda yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane sama da dubu guda a lokacin.

A shekarar 2016 kungiyar ISWAP ta sanar da nada Al Barnawi a matsayin jagoran ta wanda kafin nan Abubakar Shekau ne ke jagoranci.

Tsohon shugaban boko haram Abubakar Shekau
Tsohon shugaban boko haram Abubakar Shekau Handout BOKO HARAM/AFP/Archivos

Kafin sauke Shekau daga jagorancin kungiyar ya bayyana goyan bayan sa ga kungiyar IS a watan Maris na shekarar 2015, tare da kashe dubban mutane sakamakon kai hare hare a garuruwa daban daban da jikkata mutane da kuma lalata kadarori daban daban.

Kawar da shi daga jagorancin kungiyar a shekarar 2016 ya bada damar nada Al Barnawi a matsayin sabon jagora da kuma raba mayakan kungiyar zuwa gida biyu.

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya tace an nada Al Barnawi ya jagoranci kungiyar a Yankin Tafkin Chadi ne saboda hukunta Shekau wanda ya sabawa  dokokin ta da kuma ci gaba da samun goyan bayan mayakan kungiyar da suke tare da manufofin mahaifin sa Muhammad Yusuf.

Tubabbun mayakan boko haram dake neman afuwa
Tubabbun mayakan boko haram dake neman afuwa © Daily Trust

Jaridar tace rahotanni sun ce kungiyar ISIS ce ta horar da Al Barnawi kafin ya zama shugaban ISWAP, yayin da ya kaddamar da zafafan hare hare, ciki harda wadanda suke kaiwa sansanonin soji a Yankin Tafkin Chadi, yayin da ya kaddamar da manufofin kawar da tasirin Shekau.

Bayanai sun ce Al Barnawi ya mallaki yanki mai girma a arewacin jihar Borno, inda ya sanya haraji akan mazauna wurin, yake kuma tara kudi sosai daga aikin kamun kifi, bayan taimakon da yake samu daga kungiyar ISIS.

Kungiyar BBOG dake fafutukar kubutar da 'Yam matan Chibok da mayakan boko haram suka kwashe
Kungiyar BBOG dake fafutukar kubutar da 'Yam matan Chibok da mayakan boko haram suka kwashe . AFP/Archivos

Rahotanni sun ce mayakan Al Barnawi sun lalata sansanonin soji da dama a Dikwa da Monguno da Abadam da kuma Marte dake Jihar Borno da kuma Geidam dake Jihar Yobe, tare da kafa sansani a Tafkin Chadi inda yake kai hari Najeriya da Nijar da Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.