Isa ga babban shafi
Najeriya - Yobe

Najeriya na bincike kan zargin kashe fararen hula da jirgin yaki yayi a Yobe

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta sanar da fara bincike kan rahotannin da ke cewa wani jirgin yakin ta ya kashe fararen hula bisa kuskure a hare-haren da ya yi nufin kaiwa kan mayakan Boko Haram a arewacin jihar Yobe.

Wani jirgin yakin rundunar sojin saman Najeriya.
Wani jirgin yakin rundunar sojin saman Najeriya. © The Guardian Nigeria
Talla

Mazauna kauyen Buhari da ke gundumar Yunusari a kusa da kan iyaka da Nijar, sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutane 10 ne suka mutu yayin da wasu akalla 19 suka jikkata yayin hare-haren jiragin yakin a ranar Laraba.

Kawo yanzu dai, rundunar sojin saman Najeriya ba ta tabbatar ko musanta adadin wadanda aka kashe ba, said ai mai Magana da yawunta Edward gabkwet, ya fitar da sanarwar da ke cewa, tabbas sun samu rahoto kan lamarin kuma sun kaddamar da bincike kan zargin.

Mazauna kauyen na Buhari da dama sun ce jirage masu saukar ungulu uku sun yi ta shawagi a yankin nasu, daga bisani kuma daya daga cikinsu ya bude wuta.

Wani mazaunin kauyen Grema Zanna ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, ya shaida binne mutane 10, yayin da kuma aka garzaya da wasu 22 zuwa asibiti.

Najeriya ta shafe shekaru 12 tana fama da rikicin Boko Haram da yafi shafar yankin arewa maso gabashin kasar, wanda ya yi sanadin kashe mutane sama da dubu 40 tare da raba wasu mutanen kusan miliyan 2 da gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.