Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Marwa yayi gargadi akan halarta busa tabar wiwi

Shugaban Hukumar yaki da sha da kuma safarar miyagun kwayoyi a Najeriya ta NDLEA Janar Muhammad Buba Marwa yayi gargadi dangane da masu bukatar ganin an halarta shan tabar wiwi da kuma noma ta a cikin kasar.

Shugaban Hukumar NDLEA Buba Marwa
Shugaban Hukumar NDLEA Buba Marwa © Voice of Nigeria
Talla

Marwa yace yawan ‘Yan Najeriyar dake busa tabar wiwi ya zarce yawan al’ummar kasar Portugal miliyan 10 da dubu 100 ko Girka mai miliyan 10 da dubu 700 ko kuma Jamhuriyar Benin mai mutane miliyan 12 da dubu 100.

Tsohon gwamnan Lagos ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi wajen wani bikin da ya gudana a Akure, inda yake cewa Najeriya bata da tsarin sanya ido akan masu amfani da tabar wiwin kamar kasashen da suka ci gaba, saboda haka halarta ta zai yiwa kasar matukar illa.

Marwa yace miyagun kwayoyi cikin su harda wiwi na matukar tasiri wajen aikata manyan laifuffuka a Najeriya, saboda haka yana da muhimmanci a hada karfi da karfe wajen shawo kan matsalar.

Shugaban Hukumar NDLEA yayi kuma gargadi akan mutanen da suka mayar da tabar wiwi tamkar wata alawa lura da irin illar da take yiwa jama’a, yayin da ya bayyana aniyar hukumar sa na ci gaba da yaki da masu noma ta da kuma masu amfani da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.