Isa ga babban shafi
Najeriya- tsaro

An kashe mutane 70 a Najeriya ciki harda Janar - Janar biyu a mako daya

A yayin da kalubalen tsaro ke ci gaba da tsanantaa Najeriya, akalla mutane 72, ciki har da janar janar na soji 2 ne suka mutu sakamakon hare hare na kungiyoyi masu dauke da makamai a fadin kasar a cikin makon da ya gabata.

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos
Talla

Adadin ya kunshi jami’an tsaro 12 ciki har da sojoji masu mukamin Birgediya Janar da Air Vice Mashal, a yayin da saura 61 fararen hula ne.

A binciken da jaridar ‘Premium Times da ake wallafawa a kasar ta gudanar, yankuna hudu na kasar ne suka fuskanci hare hare  banda kudu maso kudu da kudu maso yammacin kasar.

 Yankin Arewa maso yammmacin kasar ne ya fuskanci mafi akasarin hare haren, sai yankin arewa maso gabashin kasar ke biye.

Wannan adadi na hare hare 11 rasa rayuka 72 na njuni da cewa lamarin na makon da ya gabata zarta na makon da ya gabace, wanda aka kai hare hare 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.