Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Sojojin Najeriya na shirin amfani da jiragen Super Tucano akan 'Yan bindiga

Bayyana ‘Yan bingidar Najeriya da suka hana mutane zaman lafiya a matsayin ‘yan ta’adda zai baiwa rundunar sojin kasar damar amfani da jiragen yakin Super Tucano da aka sayo daga Amurka domin barin wuta akan su.

Jiragen yaki samfurin  Super Tucano
Jiragen yaki samfurin Super Tucano embraerdefensesystems.com/
Talla

Rahotanni sun ce daga cikin sharidodin da Amurka ta gindayawa Najeriya kafin sayar mata da jiragen shine ba za’ayi amfani da su akan fararen hula ba, sai ‘Yan ta’addan da suka addabi kasar irin su boko haram.

Hukuncin da alkali Taiwo Taiwo na babbar kotun Abuja ya yanke na ayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda yanzu zai sauya matsayin sojojin da kuma basu damar afkawa musu da sabbin jiragen.

Yan bindiga a Najeriya
Yan bindiga a Najeriya © Daily Trust

Gwamnatin Najeriya ce ta bukaci kotun da ta amince wajen bayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda lura da irin kisan da suke yiwa fararen hula ba tare da kaukautawa ba da kuma sace dukiyoyin su.

Mai gabatar da kara na tarayya Mohammed Abubakar yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin shigar da karar domin bayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda.

Sojojin Najeriya dake yakar kungiyar Boko Haram
Sojojin Najeriya dake yakar kungiyar Boko Haram AFP/SUNDAY AGHAEZE

Alkali Taiwo ya kuma bada umurnin haramta duk wani yunkuri ko alaka da yan bindigar dake aikata irin wadannan laifuffuka, yayin da ya umurci gwamnatin tarayya da ta wallafa umurnin na sa a manyan jaridun kasar guda biyu.

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Najeriya Janar Bernard Onyeuko ya bayyana umurnin kotun a matsayin mataki na farko, yayin da yace nan bada dadewa ba zasu sanar da jama’a irin matakan da zasu dauka.

Rahotanni daga Najeriya sun ce dubban mutane suka mutu sakamakon hare haren ‘Yan bindigar a yankin arewa maso yamma da kuma arewa ta tsakiya.

Wannan ya sa majalisar tarayya ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda lura da irin illar da suka yiwa zaman lafiya wajen kashe jama’a baji ba gani da kuma tada garuruwa da dama, yayin da sace mutane domin karbar diyya ya zama ruwan dare game duniya a yankunan biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.