Isa ga babban shafi
Najeriya - Edo

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da DPO sun nemi naira miliyan 50

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da Ibrahim Aliyu Ishaq, DPO na ‘Yan Sandan dake kula da karamar hukumar Etsako ta Tsakiya dake Jihar Edo a Najeriya, sun bukaci a biya su diyyar naira miliyan 50 kafin su sake shi.

Hoto domin misalin 'yan bindiga a Najeriya.
Hoto domin misalin 'yan bindiga a Najeriya. Jakarta Globe
Talla

Rahotanni sun ce an sace baturen ‘Yan Sandan ne a karshen mako lokacin da yake tafiya a cikin motarsa akan hanyar Auchi zuwa Agenebode.

Ya zuwa yanzu rundunar ‚Yan Sandan Jihar bata ce komai dangane da bukatar ‚Yan bindigar ba.

Satar mutane domin kudin fansa da kuma kai hare-hare tare da kisan mutane da cin zarafinsu da ‚yan bindiga ke yi a Najeriya na cigaba da zama matsalar dake kann gaba wajen ci musu tuwo a kwarya a sassan kasar, musamman ma a yankin arewa maso yammacin kasar.

A watannin baya bayan nan ne kuma, lamarin yayi kamari inda, ‘yan bindigar suka rika afkawa makarantu suna sace dalibai da malamansu, lamarin da ya kai kan jami’an tsaro a yanzu.

Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Agustan da ya gabata, gungun ‚yan bindiga suka kai farmaki kann makarantar da horas da hafsoshin soji ta NDA dake jihar Kaduna, inda suka sace babban jami’in soji 1 gami da sanadin mutuwar guda biyu, koda yake daga bisani a ceto jami’in tare da hakala wasu daga cikin ‚yan bindigar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.