Isa ga babban shafi
Najeriya

Dakarun Najeriya sun halaka mayakan ISWAP fiye da 20 a Rann

Dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar kashe mayakan ISWAP akalla 24 a garin Rann dake jihar Borno a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Wasu sojojin Najeriya a garin Marte dake arewa maso gabashin Najeriya.
Wasu sojojin Najeriya a garin Marte dake arewa maso gabashin Najeriya. AP - Jon Gambrell
Talla

Bayanai sun ce  ‘yan ta’addan sun gamu da gamonsu ne, bayan da suka yi yunkurin afkawa sansanin sojojin Najeriyar dake garin na Rann, wanda mayakan Boko Haram suka daidaita a shekarun baya.

Wata majiya ta ce yayin fafatawar dai sojin Najeriya sun rasa dakarunsu guda bakwai.

Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sadarwa zamani ya nuna gawarwakin mayakan na ISWAP da dakarun Najeriya suka halaka, gami da muggan makaman da suka kwace daga hannunsu.

A wani labarin kuma, rahotanni daga Jihar ta Borno sun ce wasu da ake kyautata zaton mayakan ISWAP ne sun harba rokoki zuwa wasu sassan garin Maiduguri, lamarin da yayi sanadin rushewar wasu gine-gine.

Sai dai kawo yanzu babu rahoton samun hasarar rai, a yayin da jirgin sojin Najeriye ke shawagi domin tabatar da tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.