Mayakan ISWAP sun kashe dakarun Najeriya 18 a Maiduguri
Akalla sojojin Najeriya 16 mayakan k’ungiyar ISWAP suka kashe lokacin suka y iwa tawagar motocinsu kwanton bauna a jihar Borno.
Wallafawa ranar:
Harin na ranar Laraba shine mafi muni da k’ugiyar ISWAP ta kai a kan sojojin Najeriya a cikin wannan shekarar tun da aka fara hare haren ta’adanci.
'Yan kugiyar IS din dai sun tada bama bamai tare da budewa rundunar sojin wuta ne yayin da suke kan hanyar dake tsakanin Maiduguri da Mangono, abin da ya yi sanadiyar mutuwar sojoji 18 da ‘yan sa kai guda 2, yayin da mayakan suka yi garkuwa da sojoji 2.
Sha daya daga cikin tawagar sojojin sun jikkata a harin, sannan motocin su da dama aka kona, a cewar wani soja da ya nemi a sakaya sunansa saboda rashin ba shi da izinin zantawa da manema labarai ba.
Tuni kungiyar ISWAP ta dauki alhakin kai harin kuma ta ce sojoji 25 ta kashe a cewar masu bibiyar kafarsu
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu