Isa ga babban shafi
NAJERIYA-TSARO

Ku dinga yi wa gwamnatinmu adalci - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar kasar ta shiga matakin karshe na yaki da kungiyar boko haram, yayin da ya sha alwashin murkushe su tare da yan bindigar da suka hana zaman lafiya a yankin arewa maso yammacin kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Maiduguri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Maiduguri © Nigeria presidency
Talla

Buhari yace yana sane da nasarorin da suke samu a matsayin gwamnati a arewa maso gabas da kuma koma bayan da suke samu a arewa maso yamma, inda mutanen da suka fito daga wuri guda da al’ada guda ke afkawa junan su suna sace dukiya da kuma kashe junan su.

Shugaba Buhari da Gwamna Zulum sun karbar gaisuwa daga dalibai a Maiduguri
Shugaba Buhari da Gwamna Zulum sun karbar gaisuwa daga dalibai a Maiduguri © Nigeria presidency

Shugaban yace tuni ya bada odar sayo jiragen saman yaki da manyan makamai daga Amurka tare da motocin yaki wadanda za’a kaddamar da su akan irin wadannan mutane da suka hana zaman lafiya a Najeriya.

Buhari wanda ya baiwa sojoji umurnin afkawa ‘yan bindiga a jihohin Zamfara da Sokoto yace ba zasu ragawa wadannan mutanen ba, saboda irin illar da suke yiwa jama’a.

Shugaban kasar ya bukaci ‘Yan Najeriya da su yiwa gwamnatin sa adalci, lura da yadda suka samu kasar lokacin da suka karbi mulki da kuma yadda take ayau.

Buhari na yiwa sojoji jawabi
Buhari na yiwa sojoji jawabi © Nigeria presidency

Buhari yace mutanen arewa maso gabas sun fi kowa sanin halin da ake ciki lokacin da ya karbi mulki, kuma sun bayyana haka wajen irin tarbar da suka masa.

Shugaban yace da zaran wa’adin mulkin sa ya kare zai sauka daga karagar mulki kamar yadda yayi alkawari lokacin da ya rantse da Al Qur’ani cewar zai mutunta kundin tsarin mulki, saboda haka nan da watanni 17 da ikon Allah zai sauka daga mulki domin baiwa wanda zai gaje shi damar dorawa daga inda ya tsaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.