Najeriya-Bauchi
Al'ummar yankunan Bauchi sun razana da bakon jirgin sama dake musu shawagi
Al’ummar garuruwan da ke kewayen dajin Lame/Burra da ya yi iyaka da jihohin arewa maso yammacin Nigeria da kuma jihar Bauchi, sun yi shelar ganin yadda wani jirgi mai saukar ungulu da ba a san asalinsa ba, ke yawaita shiga yankin nasu ba zato ba tsammani.Wannan kuka na su, ya zo daidai lokacin da Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad, shi ma ya jawo hankalin hukumomin tsaron Nigeria game da wannan batu.Wakilinmu Ibrahim Malam Goje, ya aiko mana wannan rahoto daga Bauchi.
Wallafawa ranar:
Kunna - 01:34