Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a kawo karshen matsalar karancin man fetur a mako mai zuwa - NNPC

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya bayar da tabbacin cewa zai kawar da matsalar karancin man a fadin kasar cikin mako mai zuwa.

Layin motoci a wani gidan sayar da man fetur a Abuja, babban birnin Najeriya.
Layin motoci a wani gidan sayar da man fetur a Abuja, babban birnin Najeriya. © REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Sanarwar na kunshe ne cikin bayanan da kamfanin na NNPC ya gabatarwa taron majalisar zartaswar Najeriya NEC a cikin makon nan, wanda ya gudana a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo tare da gwamnoni da kuma ministoci.

Kamfanin  bayyana cewa ta tuni ya fitar da matakan shawo kan matsalar karancin man, ciki kuwa har da samar da karin lita biliyan 2 da dubu 300.

‘Yan Najeriya a sassan kasar dai na cigaba da fama da matsalar karancin man fetur lamarin da ya haifar da cikas ga tsarin gudanar da harkokin yau da kullum a fannonin, sufuri, da kasuwanci, da ilimi da wasu ayyukan da dama.

Bayanai sun ce a birnin Abuja, ana samun  lita daya na man fetur daga hannun ‘yan bumburutu a kan Naira 700, a yayin da masu ababen hawa ke kokarin samun makamashin.

Tun a makon farko na watan Fabarairu, wannnan matsala ta kunno kai, bayan da aka gano litar man fetur din gurbatacce kusan miliyan 100 da aka shigar da shi Najeriya kunshe da sinadarin methanol mai kassara injunan ababen hawa, abinda ya sanya aka dakatar da sayar da man da zummar maida shi ga wadanda suka saidawa kasar.

A ranar Talata ne kuma kamfanin kula da albarkatun man Najeriya na NNPC ya fitar da sanarwa da ta ce ya kaddamar da aikin tsawon sa’o’i 24 a dukkanin cibiyoyinta da gidajen sayar da man fetur domin kawo karshen matsalar karancinsa.

Kamfanin na NNPC ya ce yanzu haka yana da litar man fetur mai inganci sama da biliyan daya wanda tuni ya fara aiki tukuru wajen wadata ‘yan Najeriya da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.