Isa ga babban shafi
Najeriya - Kebbi

'Yan bindiga sun sace mutane da dama a Yawuri bayan kashe wasu fiye da 10

Rahotanni daga jihar Kebbi a arewacin Najeriya sun ce, ‘yan bindiga sun kashe mutane 15 tare da yin awon gaba da wasu da ba a san adadinsu ba a wasu yankuna dake karamar hukumar Yauri.

Yan bindiga a Najeriya
Yan bindiga a Najeriya © Daily Trust
Talla

Wani magidanci dake daya daga cikin yankunan da al’amarin ya faru ya shaida wa sashin Hausa na RFI cewa, tun da misalin karfe 6 na safiyar Asabar ne barayin dajin suka afkawa garuruwan Kimoh, Hantsi, Birnin Yauri da Gwalam6o, inda suka tarwatsa al’umma.

Ya ce ganin haka ne ya sa mutane suka bazama cikin dazuka don tsira da rayuwarsu, amma ‘yan bindigar suka bi su da harbi da sara, inda suka kashe da dama daga cikinsu.

Yanzu dai al’ummar sun gano gawarwakin mutane 15, cikinsu har da mata, sai dai sun ce ‘yan bindigar da yanzu haka ke cikin dajin sun hana su dauko sauran gawarwakin ‘yan uwan nasu.

Al’ummar yankunan, wadanda suka ce su na neman dauki na gaggawa, sun koka kan yadda jami’an tsaro ke sintiri a kan tituna ba tare da sun yunkura wajen farauto ‘yan bindigan da suka yi awon gaba da dimbim mutanesu da dabbobinsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.