'Yan bindiga sun aurar da 13 daga cikin dalibai mata na Birnin Yauri
Watanni 8 bayan da ‘yan bindiga suka yi awon gaba da daliban sakandiren gwamnatin Tarayyar Najeriya ta birnin Yauri a jihar Kebbi, har yanzu ‘yan bindigar suna rike da fiye da 10 daga cikinsu, duk kuwa da biyan kudin fansa da aka yi, da kuma musayar fursunoni da aka yi a lokuta dabam dabam.
Wallafawa ranar:
Wani bincike da jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa a Najerya ta gudanar na nuni da cewa an aurar da kimanin dalibai mata 13 ga ‘yan bindiga, kuma yanzu haka wasu daga cikinsu na da juna biyu.
A ranar 17 ga watan Yunin shekarar da ta gabata ne barayin dajin da ke biyayya ga kasurgumin dan bindigar nan, Dogo Gide suka afka wa makarantar sakandiren Birnin Yauri a jihar Kebbi, inda suka yi awon gaba da gwamman dalibai da malamai 5.
Binciken da jaridar ‘Daily Trust’ ta gudanar ya nuna cewa tsakanin dalibai 11 zuwa 14 na hannun ‘yan bindigar, kuma daya ne kawai namiji daga cikinsu.
Wasu majiyoyi sun ce tabbas Dogo Gide ya aiwatar da barazanar da ya yi ta aurar da ‘yan matan da suka rage a hannunsa, inda yanzu haka wasu daga cikinsu na da juna biyu.
Wani wanda aka gudanar da tattaunawar sako daliban Yaurin da shi, ya shaida wa jaridar ‘Daily Trust’ cewa ko a tsakiyar watan Janairu an saki wasu ‘yan mata 3, amma da juna biyu suka dawo gun iyayensu.
Har yanzu gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce tana iya kokarinta na ganin an kubutar da daliban da suka saura a hannun ‘yan bindiga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu