Isa ga babban shafi
Kebbi-Ta'addanci

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro 19 a jihar Kebbi

‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 19 a jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya kwanaki kalilan bayan kisan ‘yan sa kai 66 a kauyen Anene, yayin wani farmaki na daban da 'yan bindigar suka kai.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Majiyar tsaro daga jihar ta Kebbi sun bayyana cewa cikin jami’an tsaron da ‘yan bindigar suka kashe har da Sojoji 13 da kuma ‘yan sanda 5 baya ga dan sakai 1.

Bayanai sun ce da yammacin jiya talata ne ‘yan bindigar suka farmaki kauyen Kanya da ke makwabtaka da Anene wanda suka farmaka a litinin din nan dukkaninsu a karamar hukumar Sakaba.

Hare-haren 'yan bindiga tare da garkuwa da mutane don neman kudin fansa ba sabon abu ba ne a jihar ta Kebbi da ke yankin Arewa maso yammacin Najeriya wanda a lokuta da dama ke sabbaba asarar rayukan tarin mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.