Isa ga babban shafi
Najeriya-Ta'addanci

ISWAP ta dauki alhakin kisan 'yan sanda a Kogi

Kungiyar IS ta yankin yammacin nahiyar Afrika da ake kira ISWAP ta dauki alhakin harin da aka kai wani ofishin ‘yan sanda da ke karamar hukumar Okene ta jihar Kogi da ke Najeriya.

Wasu daga cikin motocin da sojojin Najeriya suka kwato daga hannun mayakan Iswap
Wasu daga cikin motocin da sojojin Najeriya suka kwato daga hannun mayakan Iswap AUDU MARTE / AFP
Talla

Da safiyar Asabar ce wasu ‘yan bindiga suka kai hari ofishin ‘yan sanda, kamar yadda kakain rundunar ‘yan sandan jihar Williams Aya ya tabbatar.

Aya ya ce maharan sun bullo ta bayan ofishin, inda suka yi ta harbi ba kakkautawa, lamarin da ya kai ga rasa jami’an ‘yan sanda 3, amma kuma su ma ‘yan ta’addan sun tsere da raunukan harbn bindiga.

A wani sakon manhajar Telegram,  kungiyar ISWAP ta dauki alhakin kisan ‘yan sandan da ta ce sun kai 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.