Isa ga babban shafi
NAJERIYA - ISWAP

Rundunar MNJTF ta kashe mayakan ISWAP sama da 100 a Tafkin Chadi

Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100, cikinsu har da manyan kwamandoji 10, a cikin 'yan makwannin da suka gabata, yayin hare-hare ta sama da ta kasa a yankin tafkin Chadi.

Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100.
Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100. © MNJTF
Talla

Kakakin rundunar sojin hadin gwiwar ta kasa da kasa, Kanar Mohammed Dole, ya ce dakarunsu da suka kutsa cikin yankunan da masu tayar da kayar bayan ke iko da su a yankin tafkin na Chadi, sun samu nasarar kwace makamai masu yawan gaske, da kayayyakin abinci da kuma miyagun kwayoyi.

Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100.
Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100. © MNJTF

Kanar Dole ya kara da cewar, sojoji 18 ne suka samu raunuka yayin artabu da mayakan na ISWAP wadanda suka binne bama-bamai a gefe hanya, sai dai kanar din bai yi karin bayani kan ko an samu wasu dakarun da suka rasa rayukansu ba.

Dole dai bai bayar da lokacin aikin ba ko adadin sojojin da aka kashe amma ya ce sojoji 18 ne suka jikkata sakamakon wasu bama-bamai da aka binne ta hanyar ja da baya.

Mayakan Boko Haram da kungiyar da ta balle daga yankin yammacin Afirka (ISWAP) sun shafe fiye da shekaru goma suna fafatawa da sojojin Najeriya a wani rikici da ya barke a jihohin da ke makwabtaka da kasar.

Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100.
Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100. © MNJTF

Rikicin masu kaifin kishin Islama ya ta'allaka ne a yankin arewa maso gabashin Najeriya kuma ya yi sanadin mutuwar dubban mutane yayin da suke korar miliyoyin mutane daga gidajensu zuwa sansanonin 'yan gudun hijira.

Amurka zata saidawa Najeriya jiragen yaki

Najeriya ta samu karbuwa bayan Amurka a makon jiya ta amince da sayar da makamai kusan dala biliyan daya. ‘Yan majalisar dokokin Amurka sun dage yarjejeniyar ne saboda nuna damuwarsu kan yiwuwar cin zarafin bil’adama daga gwamnatin Najeriya. kara karantawa

Kungiyar Boko Haram dai ta kasance a kafar baya tun bayan mutuwar shugabanta, Abubakar Shekau, a shekarar da ta gabata a watan Mayu, a yakin da ta yi da kungiyar ISWAP Najeriya ta ce dubban mayakan Boko Haram da iyalansu ne suka mika wuya tun bara.

Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100.
Sojojin hadakar da ke karkashin rundunar hadin gwiwa ta MNJTF daga Najeriya da Nijar da kuma Kamaru sun samu nasarar kashe mayakan ISWAP fiye da 100. © ©MNJTF

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.