Isa ga babban shafi
Najeriya-IPOB

Najeriya ta bukaci Birtaniya ta murkushe masu daukar nauyin IPOB

Fadar gwamnatin Najeriya ta yi na’am da matakin Birtaniya na amincewa da sanya kungiyar IPOB mai neman kafa kasar Biafra a cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda da ta yi.

  Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya.
Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Mai magnada yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a daren Jiya Juma’a, ina yake cewa mataki na gaba da Birtaniya ya kamata ta dauka shine sanya takunkumai ta wurin karbe kadarorin kungiyar tare da rufe kafofin sadarwarta da kuma soke bai wa masu daukar nauyinta bizar shiga kasar.

Kakakin na shugaban Najeriya ya ce irin wadannan takunkumai sun taka rawa wajen taka wa wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda birki.

‘Yan bindiga da ake zaton ‘yayan kungiyar IPOB ne, sun tsananta aikata ta’asa a yankin kudu maso gabashin Najeriya a baya bayan nan.

Yanzu haka dai shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu yana tsare a hannun hukumomin Najeriya, inda yake fuskantar tuhumar cin amanar kasa da sauran tuhume-tuhume.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.