Adadin Mutanen da suka mutu a Fashewar Kano ya kai 9
Adadin wadanda suka mutu sakamakon fashewar da ta afku a Sabon Gari a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano da safiyar Talata, ya karu zuwa tara, kamar yadda Ma'aikatar Agaji ta gwamnatin Tarayya ta sanar a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.
Wallafawa ranar:
Kunna - 01:37
Da farko dai Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da samun fashewar wani abu mai kara a unguwar Sabon Gari amma tace hadarin bai shafi makarantar dake kusa da wurin ba, yayin da rahotanni suka ce mutane 3 suka mutu sakamakon hadarin.
Sanarwar da Kwamishinan yada labarai Muhammad Garba ya gabatarwa manema larabai tace an samu fashewar ce a wani shagon sayar da abincin Kaji dake daura da makarantar dake titin Aba Road a unguwar Sabon Gari dake karamar hukumar Fagge.
Kwamishinan yace yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin tantance abinda ya haddasa hadarin da illar da yayi, an bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalin su da kuma baiwa gwamnati da jami’an tsaro damar gudanar da ayyukan su.
Shaidun gani da ido sun ce akalla mutane 3 suka mutu sakamakon hadarin, yayin da wasu kuma suka samu raunuka.
Wikilin RFI Hausa
Wakilinmu RFI Hausa a Kano Abubakar Isa Dandago ya ji ta bakin shugaban Yan kasuwar Sabon Gari wanda ya tabbatar masa da samun fashewar, yayin da jami'an aikin agaji ke aiki domin taimakawa wadanda hadarin ya ritsa da su.
Rundunar sojin saman Najeriya ta soke bikin da ta shirya gudanarwa a Kano saboda hadarin da aka samu, yayin da jami'an tsaro suka yi harbi sama domin tarwatsa bata gari dake kokarin amfani da hadarin da aka samu domin satar kayan jama'a.
Kuna iya latsa alamar sauti domin sauraron rahoton Abubakar Isa Dandago.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu