Isa ga babban shafi

Victor Osimhen za ya taka muhimmiyar rawa a Super Eagles -NFF

Hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta dawo da dan wasan gabar kungiyar Victor Osimhen da nufin buga gasar cin kofin Afrika na shekara ta 2023 a wasar da kungiyar ta Super Eagles za ta yi da kungiyoyin  kwallon kafar Sierra Leonne da Sao Tome Principe.

Wasu magoya bayan kungiyar kwallon kafar Najeriya super eagle yayin wasan da aka fafata tsakanin Ghana da Najeriya a Abuja
Wasu magoya bayan kungiyar kwallon kafar Najeriya super eagle yayin wasan da aka fafata tsakanin Ghana da Najeriya a Abuja © NFF
Talla

Dan wasan mai shekaru 23 na daga cikin yan wasan  Super Eagles da ba su halarci wasanni sada zumunta da wannan kungiya ta yi a Amurka, aka kuma sake gayyato su yanzu haka.

Osihmen na fatan zarce Yekini

Dan wasan gaban Napoli kuma dan Najeriya Victor Osimhen ya bayyana aniyarsa na zarce irin banjintar da Rashidi Yekini ya yi a wajen cin kwallaye a babbar tawagar kwallon kafar kasarsa ta Super Eagles duk da cewar 'kamar da wuya'.

Wasu daga cikin yan wasan da hukumar ta gayyato sun hada da Ahmed  Musa,Leon Balogun,Zaidu Sanusi da mai tsaron gida Adebayo Adeleye,Sadiq Umar da Shehu Abdullahi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.