Eguavoen ya ajiye aikin rikon kwaryar horas da Super Eagles
Augustine Eguavoen ya ajiye mukaminsa na kocin rikon kwaryar tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles.
Wallafawa ranar:
Eguavoen ya ajiye aikin ne, bayan da Super Eagles ta fice daga gasar cin kofin kasashen Afirka, bayan rashin nasara a karawarsu da Tunisia da ci 1-0 a zagayen gasar AFCON na biyu jiya Lahadi a Kamaru.
Kocin dai ya jagoranci tawagar ‘yan wasan Najeriya lashe wasanni 3 jere da juna a matakin rukuni, inda suka fara da doke Masar da 1-0, Sudan da 3-1, sai kuma doke Guinea-Bissau da 2-0, kafin su sha kaye a fafatawarsu da Tunisia.
Eguavoen ya karbi rikon kwaryar horas da Super Eagles bayan da hukumar kwallon kafar Najeriya ta kori kocin ‘yan wasan kasar Gernot Rohr a watan jiya, inda ta sanar da Jose Peseiro na kasar Portugal kuma tsohon kocin kungiyar FC Porto a matsayin sabon koci na dindindin da zai fara aiki bayan gasar cin kofin kasashen Afirka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu