Isa ga babban shafi

Oyebanji na APC ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar Ekiti

Hukumar zaben Najeriya INEC ta bayyana Abiodun Oyebanji, dan takarar jam’iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar gwamnan jihar Ekiti da aka yi a jiya Asabar.

Zababben Gwamnan jihar Ekiti Abiodun Oyebanji na jam’iyyar APC.
Zababben Gwamnan jihar Ekiti Abiodun Oyebanji na jam’iyyar APC. © Daily Trust
Talla

Kwamishinan hukumar zaben mai zaman kanta na jihar ta Ekiti, Farfesa Kayode Oyebode ne ya bayyana sakamakon da misalin karfe 3 na daren jiya wayewar garin yau Lahadi.

Bayan kammala kidaya kuri’un da aka kada, sakamakon ya nuna cewar, Oyebanji, wanda ya samu nasara a kananan hukumomi 15 daga cikin 16 na jihar Ekitin, ya samu kuri’u 187,057.

Segun Oni dan takarar jam’iyyar SPD ne ya zo na biyu da kuri’u 82,211, yayin da Bisi Kolawole na jam'iyyar PDP ya samu kuri'u 67,457.

‘Yan takara 16 ne suka fafata a zaben na ranar Asabar, inda aka kada jumillar kuri’u dubu 360,753, sai dai dubu 8,888 basu karbu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.