Isa ga babban shafi

Kotun Birtaniya ta ci gaba da tsare Ekweremadu kan safarar sassan jikin dan adam

Kotun majistire da ke Westminster a Birtaniya ta yanke hukuncin cewa David Nwamini Ukpo, wanda ake zargi da bayar da gudunmuwar koda ga ‘yar Sanata Ike Ekweremadu, shekaraunsa 21 ne ba shekara 15 ba kamar yadda yake ikirari.

Tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Ike Ekweremadu
Tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Ike Ekweremadu hopefornigeriaonline
Talla

Ekweremadu da matarsa sun gurfana a gaban kotun ne a yau Alhamis, inda suka ki amsa laifin da ake tuhumarsu da su na hada-hadar sassan jiki, yayinda aka mayar da shari’ar zuwa kotun manyan laifuka wacce ta dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Agusta.

Haka nan kuma, an bayar da umarnin a ci gaba da tsare su a gidan yari har zuwa lokacin ci gaba da sauraron shari’ar.

Kawo yanzu dai, ba za a maida shari’ar zuwa Najeriya ba, ganin yadda za a mayar da  shari’ar babbar kotun manyan laifuka.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar tarayyar Najeriya da kuma na jakadancin kasar sun halarci zaman kotun.

Daga cikin wadanda suka samu halartar, akwai tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawar kasar Eyinnanya Abaribe da tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark da tsohon karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba da kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kasashen waje, Adamu Bulkachuwa da dai sauran su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.