Isa ga babban shafi

An kama Ekweremadu a Birtaniya kan fataucin sassan dan adam

Jami’an tsaron Birtaniya sun kama tsohon mataimakin Shugaban majalisar dattijan Najeriya Ike Ekweremadu da mai dakin sa bisa zargin su da shirya fataucin wani yaro don cire sassan jikin sa.

Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan Birtaniya.
Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan Birtaniya. REUTERS/Neil Hall
Talla

Tun da fari dai jami’an tsaron Birtaniyan sun shafe sama da wata guda suna bibiyar shirin na Ekwere Madu da mai dakin sa, yayin da suke kulla yarjejeniya da asibitin da ake shirin aikin cire sassan jikin yaron.

A yanzu dai an fara tuhumar Beatrice Nwanneka Ekweremadu mai shekaru 55 da mai gidan ta kuma tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijan Najeriya Ike Ekwere Madu mai shekaru 60  da laifin hada kai don fatauncin kananan yara da kuma cire sassan jikin dan adam, da kuma bautar da dan adam.

Tuni dai hukumomi suka ce ma’auratan za su bayyana gaban kotun a yau Alhamis, yayin da yaron ke ci gaba da kasancewa karkashin kulawar gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.