Isa ga babban shafi

Zulum ya baiwa ‘yan sandan Borno gidaje 259 da sama da Naira miliyan 100

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa gwamnati ta ware gidaje 259 tare da kudin har N110m ga rundunar ‘yan sandan Najeriya dake aiki a jihar.

Gwamnan Barno Farfesa Babagana Umara Zulum tare da Shugaban 'Yan sandan Najeriya Usman Alkali a Maiduguri, 14/07/22
Gwamnan Barno Farfesa Babagana Umara Zulum tare da Shugaban 'Yan sandan Najeriya Usman Alkali a Maiduguri, 14/07/22 © governmet House Maiduguri
Talla

Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da bankin ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Borno (NPFM Bank).

Banki

An tsara bankin Microfinance ne tallafa wa kanana da matsakaitan sana’o’i ga iyalan ‘yan sanda, da ‘yan uwansu da kuma fararen hula a jihar Borno.

Bude bankin a Maiduguri ya samu halartar babban sufeton ‘yan sanda, Usman Baba Alkali.

Gidaje

Yayin bukin kaddamarwar , Zulum ya bayyana cewa rabon gidajen sama da 259 ga ‘yan sanda an yi shi ne domin diyya kan yadda gwamnati ta yi amfani da wasu filaye mallakar ‘yan sanda domin bunkasa wasu ayyukan more rayuwa a babban birnin jihar.

A cewar gwamna Babagana Zulum, Naira miliya 110 da aka ware, kashi 50% na kudin, wanda ya kai N55m, gudunmawar Borno ce ta hannun jari da nufin bunkasa ayyukan bankin a matakin farko.

Sauran kudaden N55m kuwa,  Zulum ya ci gaba da bayyana cewa, za a yi amfani da su wajen tallafa wa iyalan jami’an ‘yan sanda ta hanyoyi biyu.

Na farko, za’a yi amfani da Naira miliyan 25 don raba wa iyalan ‘yan sandan da suka mutu a bakin aiki.

Ya ba da umarnin a ajiye kudaden a asusun ajiyar yaran da jami’an ‘yan sandan da suka mutu suka bari.

'Yan sanda mata

Sauran Naira miliyan 30, inji gwamnan, za a saka shi a asusun ajiyar kudi domin tallafa wa ‘yan sanda Mata da ke aiki a fadin jihar Borno.

Zulum ya yabawa Babban Sufeton Najeriya Usman Baba Alkali bisa kaddamar da reshen bankin na Borno wanda ya ce, ya nuna yadda IGP ya ba da fifiko ga jin dadin ‘yan sanda.

Yayin jawabins jawabinsa, Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba Alkali, ya bayyana godewa Gwamna Zulum kan goyon bayan da yake baiwa rundunar ‘yan sandan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.