Isa ga babban shafi

Najeriya: INEC ta sauya sunan dan Abacha a takarar gwamna na PDP a Kano

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta a Najeriya INEC ta lika suna da kuma tantance sahihancin Sadik Wali a matsayin dan takarar gwamna jihar Kano karkashin jam’iyyar PDP.

Mohammed Sani Abatcha dan takarar neman gwamnan Kano karkahin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
Mohammed Sani Abatcha dan takarar neman gwamnan Kano karkahin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya © facebook
Talla

Wannan mataki tuni ya haifar da rudani a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar masu biyayya ga zartaswar jihar karkashin jagorancin Shehu Sagagi.

Bangarori biyu

A baya Jaridar Daily Trust ta ruwaito rikicin da ya barke a jam’iyyar PDP a Kano wanda ya kai ga gudanar da zaben fidda gwani bangarori biyu, wato ‘ya’yan tsohon ministan harkokin waje, Ambasada Aminu Wali da na marigayi tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha.

A ranar 30 ga watan Yuni, Kwamishinan zabe na jihar, Farfesa Riskuwa Shehu, ya shaida wa manema labarai a cewa hukumar ta sanya ido kan zaben fidda gwanin da Shehu Wada Sagagi ke jagoranta wanda ya samar da Abacha a matsayin dan takarar gwamna.

Amma bayan lika sunayen ‘yan takarar gwamna a fadin kasar a ranar Juma’a da ofisoshin INEC na jihohi suka yi, sunan Wali da na mataimakinsa Yusuf Dambatta aka gani a bangon ofishin INEC na jihar Kano.

Da yake mayar da martani kan lamarin, jami’in hulda da jama’a na INEC a jihar Kano, Ahmad Adam Maulud, ya ce hukumar a matakin jiha ta mika abin da sakamakon zaben fidda gwanin da ta sanyawa ido zuwa hedikwatar PDP ta kasa.

A tambaye hedikwatar PDP ta kasa

Ya ce abin da aka manna a bango ranar Juma’a wannan kuma hedikwatar jam’iyyar ta kasar ya kamata a tambaya.

"Mun aika da abin da muka yi zuwa hedkwatarmu ta kasa kuma abin da muka lika a yau (Juma'a) ya fito daga gare su kai tsaye."

“Duk wanda ke son neman karin haske ya tuntubi Cibiyar jam’iyyarsa ta kasa don samun bayanai,” kamar yadda ya shaida wa jaridar Daily Trust.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.