Duk wanda ya ce Najeriya kalau take yana bukatar gwajin kwakwalwa - Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce duk wanda ya ce Najeriya na cikin kwanciyar hankali akwai bukatar a duba shi, yana mai cewa bai kamata kasar ta kasance a inda take a halin yanzu ba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a wajen taron lacca na shekara 15 na gidauniyar Wilson Badejo a birnin Legas.
“Najeriya ba inda ya kamata ta kasance a yau bane. Idan wani ya ce babu laifi a inda muke a halin yanzu, to kuwa akwai bukatar a duba kwakwalrsa,” a cewar sa.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi zabin da ya dace a zabe mai zuwa domin a daidaita al’amura.
Ya kara da cewa, “Ko dai mu yi zabin da ya dace a 2023 domin idan muka yi zabin da ya dace za mu samu mafita.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu