Isa ga babban shafi

Kamfanonin mai a Najeriya sun ci bashin fiye da naira Tiriliyan 5

Jumullar bashin da bankuna ke bin kamfanonin mai a Najeriya ya kai naira miliyan dubu sau dubu 5 da miliyan dubu dari tara da 30 a watan Yunin da ya gabata, kamar yadda bayanai daga babban bankin Najeriya suka nuna.

Kamfanonin mai a Najeriya na halin tsaka mai wuya.
Kamfanonin mai a Najeriya na halin tsaka mai wuya. AFP/File
Talla

Bayanan bashin dai sun nuna cewar, bangaren mai na cikin ruwa ya ciwo bashin naira tiriliyan 4.28 ya yinda bangaren mai na kan da tudu, bankuna ke bin su bashin naira tiriliyan 1.65.

Wannan ya nuna samuwar karin naira miliyan dubu 250 daga jimillar bashin naira tiriliyan 5.68 da aka bayyana a watan Disamban shekarar bara.

Kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya PENGASSAN, a cikin watan Maris din ya gabata, ta yi tsokaci kan dimbin asarar da masu gudanar da harkokin man fetur da iskar gas suka yi sakamakon ayyukan masu lalata bututun mai da kuma satar sa.

Shugaban kungiyar ta PENGASSAN, Festus Osifo, ya ce tsakanin watan Oktoban shekarar bara  zuwa Fabrairun wannan shekarar, sama da kashi 90 cikin 100 na danyen mai da aka tura cikin bututun mai na kasar an lalata shi.

Hakan a cewarsa ya sanya Najeriya ta yi asarar karin kudaden shiga duk da tsadar danyen mai a kasuwannin duniya.

A farkon watan nan ne dai majalisar wakilai ta kasar, ta  yi Allah wadai da karuwar satar man fetur a Najeriya, inda ta yi gargadin cewa hakan zai iya gurgunta tattalin arzikin kasar idan har aka ci gaba da tafiya a haka.

A baya-bayan nan ne dai, rahotanni suka ce gwamnatin kasar ta bayar da kwangilar sa ido kan bututun mai ga tsohon shugaban kungiyar masu fafutukar kwato ‘yancin yankin Neja Delta, Tompolo, domin taimakawa wajen rage yawan satar mai da gurbatar muhalli da ayyukan satar mai a yankin ke haifarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.