Isa ga babban shafi

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya tsinewa masu gine-ginen akan hanyar ruwa

Gwamnan jihar Kano da ke arewacin Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya tsinewa wadanda ke gine-gine a kan hanyar ruwa, lamarin da ya yi sanadin mummunar ambaliyar da ta haddasa asarar tarin dukiya a sassan jihar.

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Kano State Government
Talla

Gwamna Abdullahi Ganduje wanda ke wannan tsinuwa yayin ziyarar da ya kai kasuwar kantin Kwari bayan ambaliyar makon jiya da ta kai ga asarar dukiyar kusan Naira biliyan 4, ya ce gine-ginen da ake akan hanyoyin ruwa ne ya haddasa ambaliyar.

Abdullahi Umar Ganduje ya ce zai ci gaba da tsinewa dukkanin masu irin wadannan gine-gine akan hanyoyin ruwa tare da umarnin rushe irin gine-ginen a ilahirin kasuwannin jihar.

Wannan ce dai ambaliya mafi muni da kasuwar ta Kantin Kwari mafi girma a jihar Kano ta fuskanta a shekarun baya-bayan nan wadda ke zuwa bayan gargadin da masana suka yi na ganin an dauki matakan yashe magudanan ruwa.

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta fitar da sanarwar gargadin da ke nuna yiwuwar sake fuskantar mamakon ruwa da ka iya kaiwa ga ambaliya a wasu jihohin arewacin Najeriya ciki har da Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.