Isa ga babban shafi

Iyaye 34 sun yiwa 'ya'yansu 48 fyade a jihohin Najeriya 13 cikin shekaru biyu

Alkaluman da wata jaridar Najeriya ta tattara sun nuna yadda iyaye 34 suka yiwa ‘ya’yan cikinsu 48 fyade cikin shekaru 2 a jihohin kasar 13 da Lagos akan gaba, lamarin da masana halayyar dan adam ke alakantawa da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Cikin shekarar 2019 kadai, hukumar HISBA a jihar Sokoto ta samu laifukan fyade fiye da 600.
Cikin shekarar 2019 kadai, hukumar HISBA a jihar Sokoto ta samu laifukan fyade fiye da 600. Daily Trsut
Talla

Alkaluman da jaridar Daily Trust ta wallafa yau asabar, sun nuna cewa cin zarafin 46, guda daya ne kawai ya shafi yaro namiji kuma a dukkanin matan da suka fuskanci wannan cin zarafi na lalata ko kuma fyade 4 ne kawai ba kananan yara ba.

Wani batu mafi tayar da hankali da alkaluman na Daily Trust, shi ne yadda bayanai ke nuna har da yarinya ‘yar watanni 15 da haihuwa cikin wadanda suka fuskanci irin wannan cin zarafin na fyade.

Jihar Lagos ce da ikan gaba a sahun jihohin da aka fi fuskantar wannan matsala ta iyaye su yiwa ‘ya’yan cikinsu fyade, inda a cikin shekaru 2 da suka gabata aka samu aikata irin wannan laifi sau 11 yayinda ake da irinsa 5 a Ondo kana Ekiti mai 4 sai Kwara 3 sannan Ogun 3 yayinda jihohin Abia, Anambra, Kano, Delta, Osun, Edo, Kebbi da Cross River ke da mutum daya-daya da suka aikata irin wannan ta’annati.

Cikin watan Agustan da ya gabata, an ga yadda wani uba da aka bayyana sunansa da Arowolo Ayodeji ya yi lalata da ‘yar cikinsa har sau 2 a jihar Ekiti wanda ya bayyana da sharrin shaidan, bayan da wasu bayanai suka nuna cewa Uban ya fara lalata da ‘yar cikin nasa tun ta na da shekaru 7 a Duniya.

Haka zalika cikin watan Fabarairu akwai rahotannin da ken una yadda wani Uba Audu Dare ya yi lalata da ‘yar sa mai shekaru 6 duk dai a jihar ta Ekiti.

A jihar Lagos ma jami’an ‘yan sanda sun kame wani Uba Sunday Julius da aka samu da lalata ‘ya’yansa mata har guda 4 masu shekaru 7 da 10 da 11 da kuma 15, wanda asirinsa ya tonu bayan mahaifiyar yaran ta kama shi.

Masanin zamantakewar dan adam Mahmuda Sarki ya alakanta rashin tarbiyya, rashin tausayi da kuma yanayin muhalli baya ga shaye-shayen miyagun kwayoyi a matsayin dalilin da ke haddasa wannan matsala.

Kiraye-kirayen daukar mataki don tabbatar da adalci ga yaran da suka fuskanci cin zarafi na ci gaba da tsananta musamman daga kungiyoyin kare da hakkin mata don ganin an hukunta iyayen da suka yi wannan aika-aika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.