Isa ga babban shafi

Ambaliya ta kashe 'yan Najeriya 372 a watanni 8 da suka gabata- NEMA

Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta ce daga watan Janairu zuwa yanzu ambaliya ta yi sanadin kisan mutane 372 a jihohin kasar 33 da birnin Tarayya Abuja alkaluman da ke sauyawa daga wanda gwamnati ta bayar a makon jiya.

Wani yanki na Najeriya da aka fuskanci ambaliyar ruwa.
Wani yanki na Najeriya da aka fuskanci ambaliyar ruwa. Reuters/路透社
Talla

A jawabin darakta Janar na hukumar Mustapha Habib Ahmed lokacin kaddamar da wasu sabbin motoci aiki ga jami’an hukumar ya ce ambaliyar ta fi tsananta a jihohin Adamawa da Jigawa da Taraba da Kano da kuma Bauchi da Neja baya ga jihohin Anambra da Ebonyi.

A talatar da ta gabata, wasu alkaluma da fadar shugaban Najeriya ta fitar ta ce ambaliyar ruwa daga Janairu zuwa yanzu ta kashe mutane 115 da kuma jikkata wasu 277 baya ga raba mutane dubu 73 da 379 da muhallansu sa jihohi 22 da Abuja.

Sai dai a jawabin babban daraktan na NEMA, Mr Mustapha Habib ya ce akwai mutane dubu 508 da ambaliyar ta shafa a jihohin kasar 33 da ya kai ga kisan mutane 371 tare da jikkata wasu 277 baya ga rushe gidaje dubu 37 da 633.

Daraktan na NEMA ya ce ambaliyar ta kashe tarin dabbobi tare da awon gaba da wasu da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.