Isa ga babban shafi

Jam'iyyun siyasa sun fara yakin neman zaben shugaban kasa a Najeriya

Yau laraba 28 ga watan Satumba ne ranar da aka sahalewa ‘yan takarar neman kujerar shugabancin Najeriya fara gangamin yakin neman zabe, don tunkarar  zaben kasar na shekarar 2023.

Wasu masu kada kuri'a a Najeriya.
Wasu masu kada kuri'a a Najeriya. REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

‘Yan takara 18 da ke neman darewa kujerar shugabancin Najeriya, za su shawo kan mutane miliyan 96 da dubu 300 don kada musu kuri’a a zaben na ranar 25 ga watan Fabarairu da nufin maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari.

Tun farko hukumar zaben Najeriya INEC ce ta ware ranar ta yau don sahalewa ‘yan takarar kaddamar da yakin neman zabensu.  

Jerin ‘yan takarar shugaban kasar da za su fafata a zaben na 2023 sun hada da Imumolen Christopher na AP kana Al Mustapha Hamza na AA sai Omoyele Sowore na AAC Kachikwu Dumebi na ADC sannan dan takarar jam’iyyar ADP Sani Yabagi tukuna Bola Ahmed Tunibu na jam’iyya mai mulki APC.

Sauran ‘yan takarar sun hada da Umeadi Chukwudi na APGA sannan Ojei Princess daga APM sai Nnadi Osita daga APP akwai kuma Adenuga Oluwafemi na BP SANNAN Peter Obi daga LP da kuma Rabi’u Musa Kwankwaso daga NNPP.

Kamar yadda kunshin sunayen ‘yan takarar da INEC ta fitar ya nuna, jam’iyyar NRM na da nata dan takarar Osakwe Johnson yayinda Atiku Abubakar ke tsayawa babbar jam’iyyar adawa ta PDP yayinda Abiola Kolawole ke yiwa PRP takara sai kuma Adebayo Adewole na SDP kana Ado-Ibrahim Abdulmalik daga YPP tukuna dan takarar jam’iyyar ZLP Dan Nwanyanwu.

Kamar yadda jadawalin hukumar INEC ya nuna, za a gudanar da zaben shugaban kasar da na ‘yan majalisun tarayya ranar asabar 25 ga watan Fabarairun 2023 kana ayi zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jiha a ranar 11 ga watan Maris wato makwanni 2 tsakani.

Ga duk wanda ya yi nasara a tsakanin ‘yan takarar 18 za a rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriyar ranar 29 ga watan Mayun shekarar ta 2023.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.