Isa ga babban shafi

Kashi 67 na matan Najeriya na fama da matsalar karancin abinci- UNICEF

Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF, ya ce kashi 67 cikin dari na matan Najeriya na fama da matsalar karancin jini, wanda masana ke alakantawa da karancin sinadarai masu gina jiki a abincin da matan ke ci lamarin da kuma ke barazana ga lafiyarsu.

Masana na alakanta rashin abincin mai inganci a matsayin dalilin da ke haddasa karancin jini ga matan Najeriya.
Masana na alakanta rashin abincin mai inganci a matsayin dalilin da ke haddasa karancin jini ga matan Najeriya. AP - Leo Correa
Talla

Wata babbar Jami’ar UNICEF kwararriya a bangaren abinci mai gina jiki, Ngozi Onuora da ke bayyana hakan a wajen wani taron horaswa game da abinci mai gina jiki, ta nuna rashin jin dadi game da yanayin ingancin lafiyar iyaye mata da kuma ‘ya’yan su.

A cewar jami'ar kashi 67 na matan Najeriya da ke fuskantar wannan matsar, suna samun tane saboda wasu dabi’u da basu kamata ba, inda ta ce akwai bukatar a rinka kula da da adadin jininsu, don kaucewa asarar rayuka.

A game da batun karancin abinci mai gina jiki kuwa, Onuora ta ce Najeriya ce ta farko a Afrika kuma ta biyu a duniya da ke da yara miliyan 17 masu fama da karancin abinci mai gina jiki, lamarin da ke barazana ga sha’anin lafiya ga kasar.

Ngozi Onuora ta ce ta hanyar bada fifiko a bangaren abinci mai gina jiki na jarirai, zai taimaka wajen inganta lafiya da girman yara tun daga mahaifa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.